ABNA24 : Da yake sanar da hakan babban jami’in hukumar ta WHO, kan ayyukan gaggawa, Michael Ryan, ya ce annobar data yadu a duk lungu da tsako na duniyar nan cikin gaggawa ta kuma kisa fiye da yadda ake tsammani, to akwai babban kalubale a gaba.
Wannan dai na a matsayin babban kira ga duniya akan darma damarar tunkarar cutar a nan gaba, duk da kokarin da masana sukayi na samar da allurar riga kafin cutar cikin kankanin lokaci.
Kawo yanzu dai mutane sama da miliyan 80 da dubu 850 ne suka harbu da cutar korona fadin duniya tun bayan bullarta a watan Disamba bara a kasar China, sai kuma miliyan 1 da dubu 767 da dari 828 data kashe a alkalumman da kamfanin dilancin labaren AFP ya tattaro.
Babban abun damuwa a yanzu shi ne sabon nau’in cutar mai saurin yaduwa da ya bulla a Biritaniya, wanda kuma yanzu haka ya yadu zuwa kasashen duniya kimanin 20.
Baya ga Biritaniya akwai Afrika ta Kudu da cen din ma aka sanar da bullar wani nau’in cutar na daban.
342/